Mu Zagaya Duniya
Wannan Sabon Shiri ne da ke tattauna Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya. Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
News & Politics 19 rész
Mu Zagaya Duniya - Shugaban Faransa ya nada sabon Fira Minista
19 perc
19. rész
Kamar yadda aka saba a kowane mako, sashin Hausa na RFI kan waiwaye kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Garba Aliyu Zaria ya soma bitar muhimman labarun ne daga Faransa, inda shugaba Emmanuel Macron ya nada sabon Fira Ministan bayan murabus din na da Edouard Philippe.
Mu Zagaya Duniya - Rikici ya mamaye jam'iyyar APC a Najeriya
20 perc
19. rész
tsuguni bata karewa Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ba, ganin yadda magoya bayan bangaren Bola Ahmed Tinubu suka bayyana rashin amincewar su da rusa kwamitin zartarwa da kuma nada shugabannin riko a karkashin Gwamna Mai Mala na Jihar Yobe.
Garba Aliyu Zaria ya duba tareda mayar da hankali ga manyan labaren mako daga nan sashen hausa na rediyon Faransa rfi.
Mu Zagaya Duniya - Annobar coronavirus ta kashe sama da mutane 438,250 a fadin duniya
20 perc
19. rész
Annobar coronavirus ta kashe mutane 438,250 a fadin duniya, bayan ta kama mutane miliyan 8, da dubu 90,290, yayin da miliyan 3 da dubu 698,500 suka warke.
A cikin sa’oi 24 da suka gabata, cutar ta kashe mutane 3,851, yayin da aka samu sabbin kamu 114,921, kuma akasarin wadanda suka mutu sun fito ne daga Amurka mai mutane 671, sai Brazil mai mutane 627 sai kuma Mexico mai mutane 439.
A nahiyar Turai kawai cutar ta kashe mutane 188,834, sai Amurka da Canada da suka yi asarar mutane 124,826, sai Gabas ta Tsakiya mai mutane 12,234 sannan Afirka mai mutane 6,792.
Garba Aliyu a cikin shirin Mu Zagaya Duniya ya duba mana halin da ake ciki a sassan Duniya tareda dubo wasu labaren can daban.
Mu Zagaya Duniya - Bitar muhimman abubuwan da suka faru a mako
20 perc
19. rész
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan lokaci ya soma ne da waiwayar halin da duniya ke ciki dangane da annobar coronavirus ta fuskokin adadin rayukan da suka salwanta, da kuma yawan wadanda suka kamu da cutar. Shirin ya koma leka jihar Sokoto a Najeriya inda 'yan bindiga suka halaka akalla mutane 75, sai kuma Kaduna inda gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufa'i ya sha alwashin kawo karshen tsarin karatun almajiranci.
Mu Zagaya Duniya - Bitar muhimman abubuwan da suka faru a makon jiya
19 perc
18. rész
Kamar yadda aka saba a kowane mako, sashin Hausa na RFI kan waiwaye kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Garba Aliyu Zaria ya soma bitar muhimman labarun ne daga birnin Kabul na Afghanistan, inda 'yan ta'adda suka kai mummunan hari kan wani asibitin kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF.
Mu Zagaya Duniya - Halin da ake cikin kan yaki da annobar COVID-19
22 perc
17. rész
Kamar kowane mako, Sashin Hausa na RFI kan waiwaye kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Bashir Ibrahim Idris ya soma bitar muhimman labarun ne da inda aka kwana kan yaki da annobar coronavirus a fadin duniya.
Mu Zagaya Duniya - Bitar muhimman abubuwan da suka faru a makon jiya
20 perc
16. rész
Kamar kowane mako, Sashen Hausa na RFI kan yi dubi game da wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Bashir Ibrahim Idris ya ba mu damar yin waiwaye a game da irin wadannan labarai cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya'.
Mu Zagaya Duniya - Wasu daga cikin muhimman labarai na abubuwan da suka faru a duniya
18 perc
15. rész
Kamar kowane mako, Sashen Hausa na RFI kan yi dubi game da wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe.
A wannan karo ma, Garba Aliyu Zaria zai ba mu damar yin dubi a game da irin wadannan labarai cikin shirin Mu Zagaya Duniya.
Mu Zagaya Duniya - Halin da ake cikin kan cutar coronavirus a duniya
21 perc
14. rész
Shirin Mu Zagaya Duniya na wanann mako tare da Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali ne kan cutar coronavirus wadda ke ci gaba da addabar kasashen duniya tare da lakume dubban rayuka.
Mu Zagaya Duniya - Muhimman labaran abubuwan da ke faruwa a duniya
20 perc
13. rész
Kamar kowane mako, Garba Aliyu Zaria na duba mana wasu daga cikin muhimman labarai da suka faru da wadanda ke faruwa a sassan duniya, A wannan mako mako ma ya yi tsamo wasu daga cikin irin wadannan labarai a cikin shirin ''Mu Zagaya Duniya''.
Mu Zagaya Duniya - Muhimman lamurran da ke faruwa a duniya wannan mako
20 perc
12. rész
Kamar kowane mako, Garba Aliyu Zaria kan yi dubi a game da muhimman batutuwan da suka faru a duniya cikin wannan mako da ya kawo karshe.
Mu Zagaya Duniya - Coronavirus ta lakume rayuka fiye da dubu 20
20 perc
11. rész
A kasashen Duniya an samu rudani dangane da cutar Coronavirus, wasu kasashe da suka hada da jamhuriyar dimokiradiyar Congo an ruwaito manyan jami’an gwamnati da dama na dauke da cutar cikin su harda ministan tattalin arziki Acacia Bandubola wanda kanin sa dake rike da mukamin mataimakin Darekta Dedie Bandubola ya mutu sakamakon kamuwa da cutar.
A Kenya gwamnatin Uhuru Kenyatta ta tilasta killace Mataimakin Gwamnan Kilifi Gideon Saburi wanda ya koma gida bayan ya ziyarci Jamus ba tare da killace kan sa ba.A cikin shirin mu zagaya Duniya Grba Aliyu Zaria ya dubo wasu daga cikin manyan labaren da suka mamaye Duniya kamar dai yadda zaku ji.
Mu Zagaya Duniya - Halin da annobar Coronavirus ta jefa Duniya ciki
20 perc
10. rész
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon kamar yadda aka saba yayi bitar muhimman labaran da suka auku a makon da ya kare, wanda kuma batun annobar murar Coronavirus yafi daukar hankula, la'akari da dubban rayukan da ta lakume cikin watani kalilan.
Mu Zagaya Duniya - Amurka ta ayyana dokar ta baci kan cutar Coronavirus
20 perc
9. rész
Adadin mutanen da cutar Coronavirus ta kashe ya zarta dubu 5 a sassan duniya, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Faransa ya tattaro daga alkaluman da mahukunta suka fitar.
Wannan na zuwa ne a yayin da kasar Iran ta sanar da sabbin mutane 85 da cutar aika lahira a yau Juma’a, yayin da kasashen Turai da dama suka rufe makarantu har tsawon makwanni biyu don dakile yaduwar wannan annobar.
Garba Aliyu Zaria ya duba wasu daga cikin manyan labaren Duniya cikin shirin mu zagaya Duniya .
Mu Zagaya Duniya - Halin da ake ciki kan annobar Coronavirus
19 perc
8. rész
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan lokaci dake bitar muhimman al'amuran da suka faru a karshen mako, ya soma ne da duba halin da duniya ke ciki dangane da bazuwar annobar murar mashako ta Coronavirus da kawo yanzu ta bulla zuwa kasashe sama da 90.
Mu Zagaya Duniya - Muhimman labaran karshen mako ta cikin shirin Mu zagaya duniya tare da Garba Aliyu
20 perc
7. rész
Cikin shirin Muhimman labaran karshen mako ta cikin shirin Mu zagaya Duniya tare da Garba Aliyu Zaria, ya tabo manyan labaran da suka faru a sassa daban-daban na duniya, masamman halin da ake ciki dangane da annobar cutar murar Mashako ta Coronavirus ko COVID - 19 da ta bulla a China.
Mu Zagaya Duniya - Cutar da ta barke a China na yaduwa tsakanin Bil Adama a wajen kasar.
19 perc
6. rész
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da yin kira zuwa kasashe don ganin sun dau matakan kariya daga kamuwa da cutar Mashako duk da tace babu shaidar dake nuna cewar cutar zazzabin da ta barke a China na yaduwa tsakanin Bil Adama a wajen kasar.
Wasu bayanai daga hukumomin Turai kama daga Faransa da Austria na tabbatar da bulluwar cutar a yankunan su,haka zalika a Amurka da wasu kasashen yankin Asiya.
Garba Aliyu Zaria a cikin shirin mu zagaya Duniya ya mayar da hankali a kai.
Mu Zagaya Duniya - Iran ta zargi manyan kasashen Turai da saba yajejeniyar Nukiliya
20 perc
5. rész
Iran ta zargi manyan kasashen Turai da saba yajejeniyar Nukiliya ta shekarar 2015, kwana guda bayan Birtaniya, Faransa da Jamus suka gabatar da korafin cewa Tehran ba ta mutunta yarjejeniyar.
Garba Aliyu zaria ya mayar da hankali zuwa wasu daga cikin manyen labarai na wannan mako.
Mu Zagaya Duniya - Amurka ta hallaka tsohon kwamandan Iran Qasem Solemani a Bagadaza
20 perc
4. rész
Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamna’i ya bayyana Esma’il Qaani a matsayin sabon babban kwamandan dakarun juyin juya halin kasar a kasashen ketare, bayan da a jiya juma'a Amurka ta hallaka tsohon kwamandan Qasem Solemani a Bagadaza.